Wani Malami Mai suna, Malam Muhammad Lawal Muhammad, ya yi kira ga Musulmi da su rika tallafa wa makarantun Islamiyya a cikin al’umma.
Ya yi wannan kiran ne a yayin bikin Saukar Daliban Karatun Al-Qur’ani Mai Girma na Abubakar Sadiq Memorial Islamic Centre, Phase III quarters a Unguwar Gwagwalada, Abuja, ranar Asabar.
Ya ce tun da musulmi suna son ‘ya’yansu su samu ilimin addinin musulunci, akwai bukatar iyaye su ba da tallafin kudi da na kayan aiki ga irin wadannan makarantun Islamiyya.
“Yawancinsu, a kullum musulmi suna tura ‘ya’yansu makarantun islamiyya ba tare da kula da irin wadannan makarantu ba. Idan ka lura, galibin makarantunmu ba a Basu mahimmanci a gida, saboda rashin kulawa da tallafa wa irin wadannan makarantu da malamansu,” inji shi.
Muhammad wanda shi ne shugaban taron ya ce malaman makarantun islamiyya ba kamar malaman makarantun boko ba ne wadanda a kodayaushe suke samun albashi mai tsoka, ya kuma yi kira ga iyaye da su bayar da goyon bayansu don inganta ababen more rayuwa a makarantun islamiyya.
Tun da farko, shugaban makarantar Malam Hassan Idris ya ce cibiyar ta samu yaye Dalibai 28 a shekarar 2017, bayan da suka samu ilimin share fagen karatun kur’ani mai girma da ilimin addinin Musulunci.
Ya ce jimillar dalibai 30 da suka kunshi maza 14 da mata 16, sun yi nasarar cika sharuddan kammala karatu a cibiyar a wannan shekarar.