Hukumar EFCC ta bayyana cewa, har yanzu Sanata Shehu Sani, da ake tsare dashi a ofishinta nada laifin da zai amsa na damfara da ake zarginsa dashi a gabanta.
A ranar jumma’a ne jami’in wasta labaran hukumar EFCC, Mista Tony Orilade, ya bayar da wannan sanarwar , yana mai cewa, ba wai hukumar na cin zalin tsohon dan majalisar bane.
Ya ce, lallai Sanata Sani na da tuhumar da zai amsa, kuma wadanda suke kare shi suna yin haka ne saboda rashin sanin cikakken yadda tuhumar da ke yi masa take.
Wannan sanarwa na EFCC yana zuwa bayan da wasu kungiyoyi masu zaman kansu kamar SERAP, ta bukaci a gaggauta sakin Sanatan daga kamun da hukumar take yi masa.
Shugaban kungiyar SERAP, Mista Adetokunbo Mumuni, ya zargi hukumar EFCC da karya dokokin kasa dana kasa kasa wajen cigaba da tsare tsohon dan majaliasar.