Shafin JIBWIS na Facebook sun bayyana cewa; wani makiyin Allah ya bada sanarwan cewa Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu, Wannan magana ta daga hankalin al’umma a fadin duniya, sannan mun kai karar wanda ya fara ruwaito wannan labari wajen Allah.
Sheikh Abubakar Giro Argungu yana Kasar Misrah neman magani, kuma ba’a Asibiti yake kwance ba, a gida yake zaune domin rashin lafiyar bai kai a kwantar dashi a Asibiti ba, ko yanzu munyi magana da shi ta wayar tarho, kuma har sun fara shirya-shiryen dawowa gida Naijeriya.
Dan haka a yi watsi da maganar mutuwar da ake ta yadawa.
Allah ya karawa Sheikh Giro lafiya, ya dawo mana da shi gida lafiya.