Sanata Ibrahim Shekarau (Kano ta Tsakiya) a ranar Larabar nan a zauren majalisa dattawa ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar NNPP, zuwa jam’iyyar PDP.
A ranar 29 ga watan Agusta ne Shekarau ya sauya sheka tare da magoya bayansa zuwa PDP daga NNPP, kan batutuwan da suka shafi rashin adalci da shugabancin jam’iyyar ke yi.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta wasikar inda ya bayyana sauya shekar a hukumance.
KARANTA KUMA: Shekarau Ya Bayyana Cewa Kwankwaso Ya Ci Amanarsa
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa, Shekarau a cikin wasikar ya ce ficewar sa da na dubban magoya bayansa da suka yi a Kano daga NNPP zuwa PDP, wannan don tabbatar da burinsu na siyasa ne a jam’iyyar da ta dace da su.
Bayan sanarwar, Sanatocin PDP karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Philip Aduda da kuma mataimakinsa, Chukwuka Utazi sun rungumi Shakarau kan sauya shekar zuwa jam’iyyarsu. (NAN)
A wani labarin kuma: Gwamnatin Kaduna Ta Gargadi Dalibai Da Su Dakatar Da Shirin Da Suke Yi
Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi mambobin kungiyar dalibai ta kasa da su daina shirin toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talatar nan, ya bayyana shirin da daliban da fusatar da suka yi na toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja a matsayin “ba abin yarda ba ne kuma wani share fage ne na karya doka da oda.