Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi mambobin kungiyar dalibai ta kasa da su daina shirin toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talatar nan, ya bayyana shirin da daliban da fusatar da suka yi na toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja a matsayin “ba abin yarda ba ne kuma wani share fage ne na karya doka da oda.
Rahotanni sun bayyana cewa, daliban jami’o’in da suka fusata da ke zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matakin da kungiyar malaman jami’o’in ta dauka na yajin aiki tsahon watanni bakwai, inda suka dauki matakin rufe hanyar Kaduna zuwa Abuja da ma hanyoyin isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Tashar Talabijin ta Channels ta ruwaito cewa daliban da suka gudanar da zanga-zangar a ranar Litinin din da ta gabata sun tare hanyoyin shiga filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, inda suka gurgunta al’amuran da ke cikin, inda aka sake tsai da tashin jirage da dama yayin da fasinjojin suka makale a cikin tashar jirgin sama na sa’o’i takwas.
KARANTA KUMA: Yadda Matafiya Suka Makale, Yayin Da Dalibai Suka Toshe Hanya
Daliban da suka gudanar da zanga-zangar a makon jiya sun tare hanyar Legas zuwa Ibadan Expressway da kuma titin Ibadan zuwa Ife.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufai ta gargadi dalibai da kada su tare hanyar Kaduna zuwa Abuja, yana mai cewa irin wannan mataki na iya jefa rayuka cikin hatsari.
Gwamnatin ta kuma ce hukumomin tsaro za su tabbatar da cewa ba a aiwatar da irin wannan mataki ba.
“Ta wannan sanarwar, an shawarci mutane ko ƙungiyoyin da ke shirin hana zirga-zirgar ’yan ƙasa da su daina don amfanin zaman lafiyar jama’a. Yayin da gwamnatin jihar Kaduna ba ta hana ‘yan kasa ‘yancin fadin albarkacin bakinsu ba, amma dole ne a ko da yaushe a kula da harkokin tsaro da tsaron jama’a.
“Dole ne a kuma mai da hankali sosai kan yiwuwar wasu tarukan don gudun rikidewa zuwa tashin hankali.
Don haka an shawarci ‘yan kasa da su guji shiga irin wannan jerin gwano, musamman wadanda za su yi tasiri ga al’amuran zamantakewa da tattalin arziki na sauran ‘yan kasa, ko kuma jefa rayuka cikin hatsarin da wanda ba dole ba ne.
“Za a iya tunatar da jama’a da kyau cewa ya kamata tsaro na gama gari ya kasance abin lura na farko kuma mafi muhimmanci a kowane lokaci. Don haka ana kira ga daidaikun mutane, kungiyoyi da sauran su da su lura da wannan shawarar don yin aiki sosai, ”in ji sanarwar.
El-Rufai ya umurci malaman jami’ar jihar Kaduna da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na ilimi inda ta yi barazanar bayyana matsayinsu.
NANS ta yi barazanar dakile ayyukan filayen jiragen sama na cikin gida da na kasa da kasa da kuma manyan tituna a fadin kasar nan a daidai lokacin da ake fama da rikici tsakanin Gwamnatin Tarayya da malaman da ke yajin aiki.
Gwamnatin tarayya ta maka ASUU a gaban kotun masana’antu ta kasa kuma kotun ta dage sauraron karar zuwa yau Laraba.
A wani labarin kuma: Da Ɗumi-Dumi: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aikin ASUU
Babbar kotun masana’antu ta yi kira ga kungiyar malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU da ta janye yajin aikin da take yi.
Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta shigar da kungiyar kara a gaban kotun.