A shekaru 4 da suka gabata ne a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool dake ƙasar Ingila ta bayyana Trend Alexander Arnold a matsayin wanta ta kawoshi babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Liverpool bayan daya kwashe shekaru 12 a ƙaramar ƙungiyar ta Liverpool.
Shidai Arnold ya fara buga wasa a ƙaramar ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Liverpool tun a shekarar 2004, bayan yadda yayi ƙoƙari da ƙwazo ne ya sanya aka dawo dashi babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafan.
Tun bayan shigowarsa zuwa babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Liverpool ya buga wasanni 99 inda ya sami nasarar jefa ƙwallaye guda 6. Shidai Arnold an haifeshi a ranar 7 ga watan Oktoba na shekarar 1998 inda ayanzu haka yana da shekaru 22 a duniya, inda aka haifeshi a birnin Liverpool dake ƙasar ta Ingila.
Arnold ya sami damar lashe kofuna tare da Liverpool inda daga ciki harda gasar zakarun nahiyar turai da suka lallasa Tottenham a wasan ƙarshe, sannan ya lashe kofin daya gagari Liverpool tun bayan shekaru 30 lashewa wato gasar ajin Firimiya ta Ingila inda Liverpool ta lashe gasar da maki 99 a ƙarƙashin jagorancin mai horas wa Jurgen Klopp wanda sunansa yanzu haka ya shiga kundin tarihin Liverpool.
Wannan matashin ɗan wasa yana saka riga mai lamba 66 a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool kuma shine yazo matsayi na biyu a jerin ‘yan wasan da sukafi taimakwa aci ƙwallo a kakar wasan data gabata idan aka cire Kevin De Bruyne.