Wani dan fafutuka Musa Abilewa ya damu da yadda ‘yan bindiga suka yi shiru tun bayan sakin mutane bakwai da harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya rutsa da su, inda kuma ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta shiga tsakani wajen sako sauran 42 da aka yi garkuwa da su.
Musa Abilewa, wani mai fafutukar kare hakkin jama’a kuma mai sharhi kan al’amuran jama’a, ya ce yana tsoron kada ‘yan fashin da ba su ce komai ba, kuma ba su nuna wani faifan bidiyo na sauran wadanda akai garkuwa da su ba, tun bayan sakin wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su kuma aka ce wani gwamna ne ya taimaka musu.
“An shaida mana cewa wani gwamnan daya daga cikin jihohin Arewa, da ya fahimci cewa ‘yan asalin jiharsa bakwai na cikin wadanda abin ya shafa, ya taimaka wajen sakin ‘yan asalinsa cikin gaggawa, wanda hakan ya sa wadanda ba ‘yan asalin jihar nasa ba, suke cigaba da zama a hannun yan bindigar”.
Ya ce tun da gwamnonin da suka rage ba za su ji tausayin yadda za a sako ‘yan asalin nasu ba, to dole ne gwamnatin tarayya cikin gaggawa, kuma a matsayin daya daga cikin ‘yan Nijeriya, ta gaggauta yin ceto rayuwarsu.
Ya ce duk da cewa wadanda aka sako sun shaida cewa ba a azabtar da su ba, amma dajin ba wurin shakatawa ba ne.
A karshe ya kuma yi kira ga malaman addini, da su taimaka wajen karfafa addu’o’in neman taimakon Allah a kan wadanda abin ya shafa.
A wani labarin kuma na daban.
Kungiyar Matasan Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (YOWICAN) a yankin Arewa ta Tsakiya, ta roki Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta tsawaita rajistar masu kada kuri’a da ke gudana a halin yanzu.
Owoyemi Olushola, Shugaban kungiyar YOWICAN ta Arewa ta tsakiya ne ya yi wannan roko yayin wani taron manema labarai na duniya mai taken: “Kada ku ce a’a ga Musulmi da Muslim a takarar Shugaban kasa’ a ranar Talatar nan a Abuja.
A cewarsa, ya kamata INEC ta kuma matsar da cibiyar rajistar kusa da jama’a a matakin kasa.
“Ina so in shiga cikin mabukata tare da masu korafin cewa a tsawaita aikin rajistar. Don Allah INEC ta gwada tsawaita wa’adin.
“Muna addu’a kuma muna fatan za su yi haka saboda kowa yana da ‘yancin yin rajista,” in ji shi.
Ya bukaci kowa da kowa, musamman kiristoci da su shiga zaben 2023, su zabi mutanen da suke so, su ga yadda kasar za ta inganta.
Olushola ya kuma bukace su da su rike wakilansu a matakai daban-daban.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shugaban kungiyar ya ce ya kamata INEC ta yi biyayya ga mafi rinjayen masu neman a tsawaita lokacin rajistar.
Muna fatan INEC za ta saurari bukatunmu,” inji shi.
“Muna kira ga kowane matashi da ya fito bainar jama’a don kada kuri’ar kin amincewa da hadakar kowace jam’iyya don kafa gwamnati wacce ta hada kan kasa tare da dawo da zaman lafiya. ”
Shugaban YOWICAN ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su kasance masu hankali da yin duk mai yiwuwa na dan’adam kar su haifar ko amincewa da duk wani tunanin da zai iya haifar da tsoro da rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan Najeriya. (NAN)