Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin shugabbanni a dukkani matakai a fadin kasar nan da su zamo zakaran gwajin dafi ga mabiya don ganin an cimma nasarar yaki da kalubalen da suka yi dabaibayi wa kasar.
Shugaba Buhari yanba wanna janhanaklain ne yayin Lakcha da aka shirya albarkacin bikin shekara-shekara na gidan trarihin Arewa House.
Da ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatan shi Farfesa Ibrahim Gambari, kaazalikashugaba Buhari ya bukaci yan kasa da su sanya kishin kasar a gaba sama da komai don kamar yadda mazajen jiya suka yi.
Ya jaddda bukatar cewa kyakkyawan shugabanci shine silar bude duk wata kofa ta ci gaba tare da yaki da kalubalen dake gaban kasar.
Har wa yau ya ce dgwamnatin sa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kyauatat harkar tsaro da habaka tattalin arziki gami da yaki da cin hanci da rashawa.
A bangaren shi Shehu Borno Alhaji Umar Ibn Garbai elkanemi ya ce matsalar tsaro ita ta gurguntar da harkokin tattalin arzikin yankin arewancin kasar nan inda ya bukaci mahalrta taron da su bullo da wasu dabaru da za a bi wajen tunkarar kalubalen.