Daga Sulaiman Musa
Shugaban Nijeriya, Alhaji Muhammadu Buhari, a yanzu haka na jagorantar zaman majalisar zartaswar Nijeriya (FEC) da ke gudana a Council Chambers da ke fadar shugaban kasar Nijeriya Villa, Abuja.
Wannan dai shi ne zama na farko da mambobin majalisar zartaswar suka yi tun bayan dawowar Buhari kwanaki shida da suka gabata daga ziyarar duba lafiyarsa na tsawon kwanaki 16 a kasar Landan.
Taron wanda ke gudana ta kafar sadarwar bidiyon yanar gizo, amma mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari sun bayyana a zahirance yayin zaman na yau.
Shida daga cikin ministoci suma sun bayyana a zaman na zahiri da suka kunshi ministan yada labarai Lai Mohammed; na kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed; shari’a, Abubakar Malami da ministan cikin gida, Rauf Aregbesola.
Sauran sun hada da Ministan babban birnin tarayya (FCT), Mohammed Bello, da na ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola.
Sauran kuma sun hada da shugaban ma’aikata na tarayya Dr. Folasade Yemi-Esan, da sauran mambobin majalisar kolin da suke tattauna muhimman batutuwa da suka shafi kasa a halin yanzu.
Wakilinmu ya nakalto cewa sauran ministocin kuma sun shiga zaman ne ta yanar bidiyo inda suke bayani ko sauraron ganawar da Buharin ke jagoranta
Ga hotunan zaman na yau.