Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadin data gabata ne ya sauka a birnin Washington DC domin halartar taron shugabannin kasashen Amurka da Afirka.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Buhari ya isa Joint Base Andrews da ke sansanin sojin sama da ke Maryland da misalin karfe 6.25 na yamma a agogon kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Neman Suna: Wani Mutum Ya Rikoto Daga Kan Wani Tsauni Garin Daukar Salfi Da Matarsa, Ya Rasa Ransa
Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ne ya tarbi shugaban; Jakadiyar Najeriya a Amurka, Drs Uzoma Emenike da wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Tijjani Muhammad-Bande.
Sauran jami’an diflomasiyyar Najeriya da ke kasar don tarbar shugaban sun hada da karamin jakadan Najeriya a birnin New York, Ambasada Lot Egopija da takwaransa na Atlanta, Ambasada Amina Smaila.
Buhari ya samu rakiyar Bala Mohammed da AbdulRahman AbdulRazaq, gwamnonin Bauchi da Kwara, tare da ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati.
Shugaba Buhari zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka a babban taron da za a yi tsakanin ranar Talata 13 zuwa Alhamis 15 ga watan Disamba wanda shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya kasance mai ma saukin baki.
“Gwamnatocin Afirka, kungiyoyin farar hula, al’ummomin kasashen waje a fadin Amurka, da kuma kamfanoni masu zaman kansu don ci gaba da karfafa ra’ayinmu game da makomar dangantakar Amurka da Afirka,” in ji Garba Shehu, kakakin shugaban kasar a cikin wata sanarwa.
A rana ta farko, Shehu ya ce Buhari zai yi magana a kan batun: Tsare-tsare, daidaita yanayi da kuma canjin yanayi makamashi mai adalci, inda zai tsaya kai tsaye kan bangaren “Just Energy Transition”.
Shehu ya kuma bayyana cewa shugaban na Najeriya zai kuma yi jawabi ga wasu kananan jigogi na taron da kuma halartar taron kasuwanci na Amurka da Afirka (USABF).
Ma’aikatar kasuwanci ta Amurka ce za ta dauki nauyin taron wanda ke mai da hankali kan karuwar ciniki da saka hannun jari tsakanin Amurka da kasashen Afirka.
A gefen taron kolin, kungiyar hada-hadar kasuwanci ta Afrika, za ta karbi bakuncin tawagar Najeriya a wani taron kasuwanci da zuba jari na Amurka da Najeriya.
A cewarsa, yayin taron, ana sa ran kungiyoyi da ‘yan kasuwan Najeriya za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da takwarorinsu na Amurka.
A wani labarin kuma, Tsohuwa Mai Shekaru 75 Ta Zargi Dan Uwanta Da Korarta Daga Gidan Marigayin Mijinta
Wata bazawara mai shekaru 75, Mrs. Dorothy Onwudirimba, ta zargi dan uwanta mai suna Okonkwo da korar ta da karfi daga gidan mijinta tare da lalata kadarorin gidan a ranar 6 ga watan Disamba.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, kakar ta yi zargin cewa Okonkwo ya samu umarnin kotu ne ba tare da saninta ba na lalata muhimman kadarorin gidan a garin Umuntumogu da ke karamar hukumar Okwuohia Obowo a jihar Abia.
A wani faifan bidiyo, an ga bazawarar tana kuka yayin da wasu mazaje suka cire rufin gidan suka watsar da kadarorinta a waje.