Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta tallafawa Jamhuriyar Burundi kan matsalar karancin man fetur don nuna hadin kai da ‘yan uwantaka a Afirka.
A cewar Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Buhari ya bada wannan tabbacin ne a ranar Talata 3 ga watan Janairu a fadar shugaban kasa dake Abuja, yayin da yake karbar bakoncin manzon musamman na shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye wanda ya zo da sako.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Laliga Ta Ci Taran Barcelona Kan Saba wa Dokokin Sayan Yan wasa
Adesina ya ce Buhari ya tabbatar wa Niyonzima cewa Najeriya za ta goyi bayan Jamhuriyar Burundi ta hanyoyi daban-daban kamar yadda ya kamata, bisa la’akari da hadin kai da ‘yan’uwantaka a Afirka.
Dangane da neman taimakon man fetur da shugaban kasar Burundi ya nema, shugaba Buhari ya ce ya san yadda kasar ke fama da karancin makamashi.
Bukatar Burundi na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da karancin mai tun watan Disambar 2022.
Hon Audace Niyonzima, Ministan Kudi, Kasafin da Tsare Tsaren Tattalin Arziki na Burundi, ya ce shugabansa ya aike da fatan alheri ga ‘yan Najeriya na sabuwar shekara.
“Muna addu’ar Allah ya sa zaben ya kasance cikin lumana da nasara, ta yadda Najeriya za ta ci gaba da rike sunanta a matsayin tushen zaman lafiya da kwanciyar hankali,” in ji manzon musamman na Burundi.
A wani labarin kuma, Messi Na Daf Da Tsawaita Zamansa A PGS
Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan kwallon kafa, Lionel Messi na shirin tsawaita kwantiragin shekara daya da Paris Saint-Germain a wannan makon.
Kwantiragin dan kasar Argentina na yanzu zai kare ne a karshen kakar wasa ta bana kuma an yi ta rade-radin komawarsa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, yayin da akwai wasu shawarwarin da David Beckham na Inter Miami zai iya daukarsa.