Mutane sun shiga jimamin wani boka da ya mutu bayan ya sadu da matar wani fasto a otal a Ikere Ekiti, jihar Ekiti.
Bokan mai suna Fadayomi Kehinde, wanda akafi sani da Ejiogbe, ya kama ɗaki a otal inda ya kwanta da matar wani faston garin su a ranar Litinin, 2 ga watan Janairun 2023. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA: So baya da kama: Hotunan wasu masoya sun ɗauki hankula
Bokan ya rigamu gidan gaskiya ne suna kammala saduwa da matar inda ya faɗi ƙasa rai yayi halin sa, nan da nan matar ta gaggauta sanar da ma’aikatan otal ɗin halin da ake ciki.
Abokan bokan dai sun ɗora alhakin mutuwar sa akan wani asiri da ake kira “magun” wanda magidanta ke yiwa matan su domin cutar da duk wanda ya kwanta da su.
Magoya bayan boka har dira suka yi a cocin faston inda cikin fushi suka lalata ta gabaɗaƴa.
Tuni dai aka cafke matar auren sannan aka killace ta domin gudanar da bincike da kuma kare ta daga fusatattun matasan.
Kakakin hukumar ƴan sandan jihar Ekiti, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga shafin LIB. Yace ƴan sanda sun samu rahoto daga ma’aikatan otal ɗin inda suka garzaya wurin da lamarin ya auku sannan suka tafi gawar mamacin zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwar sa.
Na Rabu Da Saurayina Saboda Bai Taba Kwanciya Da Ni Ba Tsawon Shekara 5 – Jaruma
Tsohuwar dangantakar dake tsakanin dan wasan Nollywood, Alexx Ekubo, da tsohuwar budurwar sa wacce zai aura, Fancy Acholonu, ta ci gaba da shiga kanun labarai.
Fancy kwanan nan ta fayyace komai a cikin wata hira game da abin da ya faru a cikin dangantakar su da kuma yadda babu bege na dawowa don zama tare.
Budurwar ta kuma amsa tambayoyi game da mu’amula ta aure tsakanin ta da Alexx, yadda za ta lale kuɗade a yawancin bikin auren da za’ayi.