Shugaban Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya aika da sakon ta’aziyya ga shugaban Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi bisa rasuwar matarsa Aishatu Usman Bauchi.
Shugaba Buhari ya ce ya kadu matuka da ya samu sakon rasuwar Hajiya Aishatu.
Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya jiyo shugaban kasar na cewa; Marigayiyar abin koyi ce, kuma tabbas Uwa ce wacce ya kamata a ce ta zama madubi ga iyalinta gaba daya.
A karshe shugaban kasar ya yi addu’ar Allah ya jikanta, ya kuma sanya ta a aljanna.