By Abbas Yakubu Yaura
A kalla ‘yan kungiyar ‘yan banga sama da 40 ne ake fargabar ‘yan fashi sun kashe su a karamar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi a daren ranar Litinin.
Wani dan yankin mai suna Mohammed Lawal, ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Makuku.
A cewarsa, ‘yan kungiyar ‘yan banga sun je wani samame ne a kauyen Dankolo a lokacin da suka yi wa ‘yan fashin kwanton bauna.
Ya ce, “Watakila ‘yan fashin sun samu labarin motsin ’yan kungiyar ’yan banga, don haka ne (’yan bindigar) suka yi musu kwanton bauna tare da bude musu wuta a lokacin da suke wucewa ta dajin.
“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, mun kirga gawarwakin ‘yan bangar sama da 30 da suka rasa rayukansu nan take.
“Haka kuma akwai wadanda suka jikkata daga bangaren ‘yan fashin dajin duk da cewa sun koma wurin suka kwashe gawarwakin mambobinsu.”
Lawal ya ci gaba da cewa ‘yan fashin da suka fito daga jihar Neja, sun je yankin ne domin ramuwar gayya, biyo bayan kashe mambobinsu da mutanen yankin suka yi makwanni biyu da suka gabata.
Kokarin jin ta bakin gwamnatin jihar ya ci tura, yayin da aka ce Gwamna Atiku Bagudu da mataimakansa kan harkokin yada labarai ba sa nan a jihar har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Amma shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana bakin cikinsa kan abin da ya bayyana a matsayin “mummunan kisan gillar da wasu ‘yan bindiga suka yi wa dubun-dubatar ‘yan banga a jihar Kebbi da ‘yan fashin suka yi musu kwanton bauna a karamar hukumar Sakaba/Wassagu.”
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata mai taken ‘Shugaba Buhari ya nuna bakin cikinsa kan kashe ‘yan banga a jihar Kebbi, ya bukaci a kara kaimi.
Sanarwar ta ruwaito shugaban na cewa, “Wannan muguwar daukar matakin ta’addanci abu ne mai ban mamaki kuma ina so in tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zan yi duk abin da ya kamata don magance wannan dodo da gaske.
“Babban abin da ya dame ni shi ne barazanar rayuwa da wadannan gungun ‘yan fashin daji masu kisa ke yi da kuma ’yan ta’addar da ba su da halin ko-in-kula, wadanda ko kadan ba su kula da tsarkin rayuwa.
“A yayin da nake jajanta wa iyalan wadanda wannan danyen aikin ya shafa, bari na yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga jami’an tsaron mu da su kara kaimi tare da rubanya kokarinsu domin dakile shirin ayyukan ‘yan fashi da makami tun kafin su kai farmaki. .