Wakilinmu Ibrahim Idris Abuja
Yau da Misalin Karfe 2 na Rana Shugaba Muhammadu Buhari, zai Fara gabatar da Shedar shi a Gaban Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugabancin Kasa Jim Kadan Bayan Hukumar Zabe ta Kammala Kare kanta a gaban Kotun duk da dai ba ta Gabatar da wani a Matsayin Sheda ba.
Sanarwan Hakan Ya Fito ne daga Bakin Mai Kare Shugaban Kasa da Jam’iyyar PDP, Barista Wole Olanipekun SAN, Sanarwan ta Ce Shugaba Buhari, ya Tanadi Shedu har Guda 254 domin ya kare kan sa.