Shugaba Vladimir Putin ya yi Allah wadai da takunkumin da aka kakaba wa Rasha ind akuma ya bayyana a amatsayin da “haramtacce”.
Da yake jawabi a wani taron gwamnati, Putin ya ce gwamnatocin kasashen Yamma suna yaudarar mutanensu yayin da suke yunkurin hukunta Moscow ta fannin kudi saboda kutsen da ta yi a Ukraine.
Ya kara da cewa Rasha za ta magance matsalolinta cikin nutsuwa.
A Wani labarin Kuma na daban.
Gwamnatin kasar Burtaniya ta kakabawa Mai kungiyar Kwallon kafa ta Chelsea Roman Abromovich takunkumi.
Attajirin dan kasar Rasha an daskarar da kadarorinsa kuma an hana shi yin mu’amala da daidaikun mutane da ‘yan kasuwa na kasar Burtaniya.
An kuma sanyawa Abramovich takunkumin hana tafiye-tafiye da kuma safarar kayayyaki.
Bazamu bayar da mafaka ga waɗanda suka goyi bayan mummunan harin da Putin ke kai wa Ukraine ba, inji sanarwar da Gwamnatin Birtaniya ta fitar.
Takunkumin na yau shine mataki na baya-bayan nan a cikin tallafin da Burtaniya ke bayarwa ga al’ummar Ukraine.
Har yanzu Chelsea na iya yin aiki a matsayin kungiyar ta Premier a karkashin lasisi na musamman, amma duk wani yuwuwar siyar da kungiyar da ake yi a halin yanzu ya tsaya.
Ba za a bar Blues su sake siyar da tikitin ba, ma’ana masu tikitin kakar wasa ne kawai za su iya zuwa wasannin nan gaba.
Hakanan, ba za a iya yin tautaunawar sayar da ɗan wasa ko sabonta kwantiragisa ba.