Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a fitar da Naira Biliyan 1.6 domin a tallafawa manoman citta a Najeriya
A ƙoƙarin shawo kan matsalar annobar da ta faɗawa citta wadda ta jawo hasarar citta dayawa a Najeriya musamman a Kudancin Jihar Kaduna, mai girma ministan noma na Najeriya Sanata Abubakar Kyari CON, ya ƙaddamar da kwamitin da zai kula wajen shawo kan annobar ƙarƙashin jagorancin ƙaramin ministan noma, Sabi Aliyu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Hajj: Ya kamata mu ci moriyar tikitin tikitin Musulmi da Musulmi –Sheikh Gombe ga Tinubu
Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa wannan yunƙuri ne na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an magance matsalar annobar da ta faɗawa cittar wadda ta haifar wa manoma hasarar sama da Naira Biliyan 12 a ƙasa gaba ɗaya.
Baya da haka, Minista Kyari ya ƙara da cewa shugaban ƙasa ya ba da umarnin a ware Naira Biliyan 1.6 domin a tallafawa manoman cittar waɗanda wannan iftila’i ya afkawa duba da yadda noman citta yake taimakawa ƙasa da wadataccen abinci gami da tasirin da take da shi wajen ɗaga darajar kayayyakin da Najeriya take samarwa (GDP).