Kotu ta ɗaure Sanata mai ci kan shaidar NYSC ta bogi
Wata babbar kotu da ke zamanta a Apo, Abuja, ta tasa keyar wani Sanata mai ci Benson Konbowei a gidan gyaran hali na Kuje bisa zarginsa da yin jabun takardar shedar bautar kasa, NYSC.
An gurfanar da Sanatan Bayelsa ta tsakiya a gaban mai shari’a Christopher Oba a ranar 26 ga Maris, 2024.
KARANTA WANNAN LABARIN:Hajj: Ya kamata mu ci moriyar tikitin tikitin Musulmi da Musulmi –Sheikh Gombe ga Tinubu
A cikin tuhumar mai lamba: CR/028/2023, Sufeto Janar na ‘yan sanda ya zargi Konbowei da yin damfara da wata takarda mai suna ‘Certificate of Exemption’ mai lamba 000256454 mai kwanan wata 4 ga Yuli, 2008.
Rundunar ‘yan sandan ta ce Sanatan ya aikata abin da ya saba wa tanadin sashe na 366,156 da na 158 na dokar manyar Laifuka CAP 532 ta Dokokin Tarayyar Najeriya na 1990 kuma yana da hukumci a karkashin sashe na 364 na wannan dokar.
Da aka gurfanar da shi a gaban kuliya a ranar Talata, Sanatan ya ki amsa tuhumar da ake masa.
Kotun ta ba shi damar ya koma gida tare da sanya sauraron bukatar belinsa a ranar Alhamis, 28 ga Maris, 2024.
Bayan sauraron lauyoyi a kan lamarin, kotu ta bayar da belin Sanatan kan kudi naira miliyan 50 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Mai shari’a Oba ya ce dole ne wadanda za su tsaya masu suka mallaki kadarorin da ke da takardar shaidar zama a babban birnin tarayya.
Sai dai alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare Sanatan a gidan yari na Kuje har sai an kammala sharuddan belinsa.
An dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 24, 25 da 27 ga watan Yuni
A wani labarin kuma:Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a fitar da Naira Biliyan 1.6 domin a tallafawa manoman citta
Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Kabiru Gombe, ya bukaci gwamnatin Najeriya da gwamnonin jihohin kasar da su kawo agaji ga maniyyata aikin Hajji, ya kara da cewa lokaci ya yi da za su ci gajiyar tallafin tikitin tsayawa takara tsakanin musulmi da musulmi a zaben shugaban kasa na 2023.
Ya bayyana haka ne a lokacin Tafsirin Ramadan a ranar Litinin a Abuja yayin da yake mayar da martani kan karin kudin Hajjin 2024.