Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa kasar Guinea Bissau domin halartar taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 63.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, wannan shi ne karo na biyu da Tinubu ya kai ziyara kasar waje bayan halartar taron koli kan “Sabuwar Yarjejeniyar Kudade ta Duniya” a birnin Paris na kasar Faransa, wanda shugaba Emmanuel Macron ya jagoranta.
KARANTA WANNAN: Jarabawar UTME: Ta Yi Min Karya – Mahaifin Mmesoma Ya Nemi Afuwa Kan Jabun Sakamako
Tinubu ya yi amfani da wannan damar taron wajen ziyartar tawagar Najeriya da ke kasar Guinea Bissau a karkashin rundunar tabbatar da zaman lafiya ta ECOWAS.
A nasa jawabin shugaban ya yabawa sojojin da kwamandan su Gen.Al-hassan Grema bisa sadaukarwar da suke yi wa Najeriya da kuma kasar da ta karbi bakuncinsu.
Ya kuma kara da cewa Najeriya za ta ci gaba da tallafawa dimokradiyya a yammacin Afirka da ma duniya baki daya.
“Na zo nan ne domin nuna goyon baya a gare ku. Ina so in tabbatar muku da cewa mun himmatu wajen tallafawa zaman lafiya da dimokuradiyya ba kawai a Afirka ta Yamma ba har ma a duniya baki daya.
“Najeriya kasa ce da ta yi fice a Saliyo da Laberiya da sauran wurare. Muna fatan goyon bayan ku don kare tsarin mulki.
“Na ji an biya ku alawus-alawus har yau. Babu wani abu kuma da ya kamata ya sa ku fushi. Za mu ci gaba da gina karfi.
“Muna alfahari da ku. Alfahari da amincin ku. Najeriya ta dogara da ku. Za a samu zaman lafiya da ci gaba a kasarmu,” inji Tinubu.
Grema ya bayyana jin dadin sojojin ga Tinubu saboda kasancewarsa babban kwamanda na farko a tarihin Najeriya da ya ziyarci sojojinsa a wajen gabar tekun kasar.
Yayin da yake a kasar Guinea Bissau, shugaban na Najeriya zai gudanar da tarukan kasashen biyu, da kuma wasu al’amura a gefen taron.
A cikin tawagar shugaban kasar akwai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Mukaddashin gwamnan babban bankin kasa, Dr Folashodun Shonubi; tsohon gwamna Abubakar Bagudu (Kebbi), Abdullahi Ganduje (Kano), da Abubakar Badaru (Jigawa).
Babban taro karo na 63 da za a bude ranar Lahadi, shi ne karon farko da shugaban kasar zai gudanar da taron kasa da kasa a nahiyar Afirka.
Ana sa ran shugabannin yankin 16 za su yi jawabi kan wasu batutuwan da suka shafi yankin da suka shafi tsaro, kasuwanci da mulkin dimokuradiyya kamar yadda ya shafi Mali, Burkina Faso da Guinea.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Gana Da Gwamnan Ogun
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a ranar Asabar ya gana da gwamna Dapo Abiodun a jihar Ogun.
Abiodun ne ya tarbi Shtettima ya yin da ya isa cikin jihar Ogun a filin jirgin saman Gateway International Agro-Cargo dake Iperu a karamar hukumar Ikenne a jihar Ogun.