Tinubu, wanda ya bar Abuja ranar Asabar domin ya halarci taron shugabannin kungiyar siyasa da tattalin arzikin yankin Afirika Ta Yamma ranar Lahadi,
Ana sa ran zai karbi ragamar mulki daga hannun shugaban ECOWAS na yanzu kuma shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embaló, kamar yadda majiyar diflomasiyya ta fada wa yan Jarida
Za a gudanar da zama na yau da kullun na shugabannin kasashe da na gwamnatoci karo na 63 a Bissau, babban birnin Jamhuriyar Guinea-Bissau.
A baya dai tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rike mukamin a shekarar 2018
KARANTA NANDa Dumi-Dumi: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Gana Da Gwamnan Ogun
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin zama shugaban kungiyar ECOWAS na gaba inji The Cable
Ya halarci taron koli na ‘Sabuwar Yarjejeniyar Tallafin Kuɗi ta Duniya’ wanda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shirya a birnin Paris na ƙasar Faransa a watan Yuni
Rahoton taro karo na 90 na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, na sa ran taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS zai gabatar da bayanai kan batutuwan da suka shafi kananan hukumomi
Ana sa ran zaman zai tattauna abubuwa da dama ciki har da kuma rahoto kan halin da ake ciki a Mali, Burkina Faso da Guinea
An kafa kungiyar ta ECOWAS ne a shekarar 1975 kuma a halin yanzu tana da kasashe 15 membobi da jimillar yawan jama’a miliyan 387, sannan adadin GDP ya kai na dala biliyan 816.
Kasashe mambobi sune: Benin, Burkina Faso, Cape Verde, Gambia, Ghana, Guinea, Guinea-Bissau, Ivory Coast, Laberiya, Mali, Niger, Nigeria, Senegal, Saliyo da Togo
A WANI LABARIN KUMA
Ku Gaggauta Binciken Dalilin Kona Al Kur’ani A Kasarku-Sarkin Musulmi Ga Kasar Sweden
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar ||| ya bukaci hukumomi a kasar Sweden da su gaggauta binciko tare da hukunta wanda ya kona Alkur’ani mai girma a ranar Idin babbar sallar bana
Inda yace rashin hukunta shi shaidar ce ta yaki da musulunci a kasashen Turai da ma Duniya bani daya