Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yana ziyara a yankin gaɓar tekun lardin Kwazulu_Natal , inda manyan Tituna yankin suka kasance a rufe, kuma gidaje da yawa suka lalace sanadiyar mamakon ruwan saman da aka tafka a yankin.
Yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyar ambaliyar kamar yadda mahukunta suka bayyana ya kai mutum 59, sai dai ana sa ran yawan ruwan saman ya ragu a yau Laraba.
Ana sa ran Mr Ramaphosa zai yi bayani akan matakan da gwamnati da kungiyoyin fararen hula zasu dauka wurin bayar da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa, kamar yadda Ofishin shugaban kasar ya bayyana.
Rahotanni na nuna cewa, an Sami wasu korafe-korafen sace sacen wasu kwantena a Gabar tekun, bayan awangaba da wasu kayyakin da ambaliyar ruwan yayi.
Shugaban yankin yayi Allah wadai da wannan lamari, inda yayi gargadin cewa baza su bari marasa gaskiya suyi amfani da wannan yanayi ba wurin aikata laifukan sata.