Jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa ta nada Hon. Samaila Tadawus a matsayin shugaban riko na jam’iyyar na jiha bayan murabus din tsohon shugaban jam’iyyar, Ibrahim Bilal.
Bilal dai a wata wasika mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Satumba kuma ya aika wa shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdulahi Adamu ta ofishin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a yankin arewa maso gabas ya yi murabus daga mukaminsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP Ta Nada Tambuwal A Matsayin Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa
Wasikar ta ce: “Na rubuta ne domin sanar da ku cewa na yi murabus daga mukamina na shugaban jam’iyyarmu ta APC na jihar Adamawa nan take.”
“Yayin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya bukaci na ci gaba da zama a ofishin har zuwa shekarar 2026, zan yi godiya idan har zan daina zama shugaban jihar nan take.”
“Ina matukar ba da hakuri kan duk wani rashin jin dadi da wannan labari na kwatsam zai haifar. Na gode, saboda damammakin da kuka ba ni na yi wa wannan babbar jam’iyya hidima a Jihar Adamawa. Ina so in gode muku da kaina saboda alherin ku da jagoranci.”
Bilal ya ba da tabbacin yin biyayya ga manufofin jam’iyyar ba tare da bata lokaci ba, ya kuma kara da cewa zai yi duk mai yiwuwa bisa doka don ci gaban ta.
Har ila yau, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a shiyyar Arewa maso Gabas, Salihu Mustapha, a wata wasika da ya aike wa Adamu mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Satumba, ya ce Bilal ya ajiye mukaminsa ne biyo bayan taro da tuntubar juna a dukkan matakai na jam’iyyar a jihar.
A cewarsa, ci gaba da shawarwari da tarurruka daban-daban da aka yanke a matakai daban-daban na jam’iyyar. Na rubuto ne domin sanar da ku cewa shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa Alhaji Ibrahim Bilal ya mika takardar murabus dinsa nan take.
“Saboda murabus dinsa, Samaila Tadawus (mataimakin shugaban) ya karbi mukamin shugaban riko har sai kwamitin ayyuka na kasa (SWC) na jam’iyyar ya amince da shi.”
Amma da yake magana da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, Sakataren Yada Labarai na Jihar, Hon. Mohammed Abdullahi, tare da wasu mambobin zartarwa na jihar ya ce SWC ta amince da murabus din Bilal.
Sauran ‘yan Mataimaka a taron manema labarai sun hada da shugaban riko na jiha, sakataren kungiyar na jiha, mashawarcin shari’a, shugabannin matasan jihar, da dai sauransu.
Abdullahi ya ce yayin da Bilal ya yi murabus daga jam’iyyar bisa dalilai na kashin kansa, ya kasance mai aminci, sadaukarwa da kishin jam’iyyar kuma zai gudanar da wani aiki na kasa wanda zai dace da jam’iyyar da kuma jihar.
Abdulahi ya ci gaba da cewa: “Bayan abubuwan da suka faru a ranar 5 ga watan Satumba 2022 dangane da shugabancin jam’iyyar da taruka da tuntuba daban-daban da suka biyo baya a matakin shiyya da na kasa, SWC ta gana da tattaunawa kan bayanin da shugaban jam’iyyar na jiha Alh. Ibrahim Bilal.
“SWC ta yarda da bayaninsa sosai wanda ya danganci dacewa da lokaci da kuma buƙatar saduwa da kwanan watan.”
Abdulahi ya ce SWC ta yaba da irin gudummuwar da tsohon shugaban jam’iyyar da duk masu ruwa da tsaki suka taka wajen gina jam’iyyar a jihar.
Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar za ta ci gaba da rike shi a matsayin babban mai ruwa da tsaki a jam’iyyar kuma za ta ba shi takarar mukaman jam’iyyar idan bukatar hakan ta taso.
Mai magana da yawun jam’iyyar ya ce da wannan ci gaba, jam’iyyar APC a jihar Adamawa ta ci gaba da kasancewa dunkulallen iyali da ke da muradin tabbatar da samun nasara ga daukacin ‘yan takararta a zaben da ke tafe a karkashin jagorancin shugaban riko, Tadawus.
Sai dai duk kokarin jin ta bakin tsohon shugaban jam’iyyar ta APC Bilal ya ci tura domin har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a amsa kiran waya da sakonnin tes da aka aike masa ba.
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ya Jajantawa Gwamna Akeredolu Kan Rasuwar Mahaifiyarsa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo da iyalansa bisa rasuwar mahaifiyarsu mai kaunarsu, Misis Grace Akeredolu.
Shugaban ya bayyana ra’ayinsa ne a cikin sakon ta’aziyyar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Mista Femi Adesina ya fitar ranar Juma’a a Abuja.