Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka Akinwumi Adeshina ya bukaci kasashen duniya da su taimakawa Afirka wajen bata maganin rigakafin cutar korona da kuma yafe mata bashin da ake abinta domin farfadowa daga matsalolin da annobar ta haifar.
Adeshina yace duk kokarin da kasashen duniya keyi wajen samarwa kann su maganin rigakafin ba zaiyi tasiri ba, muddin akwai wasu yankunan da basu samu maganin ba.
Shugaban bankin ya bayyana fatar sa na ganin tattalin arzikin kasashen Afirka ya sake farfadowa nan da shekaru 2 masu zuwa, inda yake cewa gaggauta samun nasarar sa na daga shirin samar da maganin rigakafin domin yiwa mazauna nahiyar allurar.
Adeshina yayi gargadi kan yunkuri watsi da Afirka wajen samun wadannan magunguna, yayin da ya jaddada muhimmanci yafewa kasashen dake nahiyar basusukan da ake bin su.