Daga: Penina Jeje Ali Damaturu
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe, Alh. Mohammed Gadaka ya taya gwamnati da ilahirin al’ummar jihar murnar bikin cikar ta shekaru 32 da kirkirar jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da rattaba hannun sakatariyar shugaban jam’iyyar ta APC, Hajiya Sa’adatu Maina sanan ta bayyana wa wakiliyar Dimokuradiyya a Damaturu.
KARANTA WANNAN: Gwamna Buni Ya Taya Al’ummar Jihar Yobe Murnar Cika Shekara 32 Da Kirkirarta
A cewar sanarwar, shugaban jam’iyyar ya yaba da kokarin gwamnati me ci ta gwamna Mai Mala Buni na kawo cigaba a jihar daya hada da samar da ababen more rayuwa da suka hada da yin hanyoyi, ingantaccen kiwon lafiya, ilimi, bunkasa noma, tsaftattacen ruwan sha, samar da aiyukan yi da sauran managartan manyan ayyuka.
Sanarwar ta kara da cewa dole a ya bawa iyayen jihar na nuna jajircewa da bada gudunmawa don ganin an samu jihar a shekaru 32 da suka gabata.
Mohammed Gadaka ya kuma yaba wa al’ummar jihar Yobe dake kasashen waje da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.
A wani labarin kuma, Ambaliyar Ruwa: Kasar Kamaru Ta Sako Ruwa daga Dam din Lagdo
Gwamnatin tarayya a daren yau 28 ga watan Agustan 2023 ta tabbatar da cewa hukumomin Kamaru sun sako ruwa daga dam din Lagdo
Ministar ta bukaci gwamnatocin jihohi da al’ummomin da ambaliyar ruwa za ta iya shafa da su fara kwashe ‘yan uwansu da dabbobinsu cikin gaggawa zuwa ga filin da ruwan bai zai shafa ba
Gwamnatin tarayya za ta samar da matsuguni na wucin gadi da sauran kayayyakin agaji ga wadanda abin zai iya shafa.
Gwamnatin tarayya a daren ranar Litinin ta tabbatar da cewa hukumomin Kamaru sun sako ruwa daga dam din Lagdo.
Gwamnatin tarayya ta kuma ce ‘yan Najeriya za su fara jin tasirin bude madatsun ruwa nan da kwanaki bakwai masu zuwa.