Daga: Penina Jeje Ali Damaturu
Shugaban Ma’aikatan Jihar Yobe, Alhaji Garba Bilal ya baiwa Kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa reshen Jihar (NUJ) gudumawar kayan wasa na “Table Tennis”.
Bilal ya bada wannan gudumawar ne a lokacin da shuwagabannin Kungiyar, karkashin jagorancin Kwamret Rajab Muhammad Isma’il suka kai masa ziyarar gaisuwa a ofishin sa dake Damaturu.
KARANTA WANNAN: Gwamna Yahaya Ya Yaba Da Gudunmawar da Sojoji Ke Bayarwa Wajen Samar Da Zaman Lafiya da Tsaro
A jawabin sa kafin ya mika gudumawar, Alhaji Garba Bilal yace wannan gudumawa ce domin tafiyar da wasannin ‘Yan Jaridu da ake shirye-shiryen yi na shekarar 2023.
Kazalika, Tawagar shuwagabannin Kungiyar ‘Yan Jaridun ta ziyarci Daraktan hukumar wasanni ta Jiha Dr. Habu Abdur-Rahman Ago da kuma mai taimakawa Gwamna na musamman a bangaren bunkasa harkokin arziki Alhaji Abdullahi Bego inda suka bada tabbacin tallafawa kungiyar domin gudanar da wasannin.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tinubu, NLC da TUC Sun Shiga Ganawar Gaggawa Kan Wani Batu
A halin yanzu gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu na ganawa da wakilan kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da kuma TUC.
Ana gudanar da taron gaggawar ne a fadar shugaban kasa dake Abuja.