Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya ce har yanzu tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa shi ne muhimmin abu ga gwamnatinsa kuma zai ci gaba da yin aiki tukuru don ganin an kiyaye shi.
Yahaya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin sabon kwamandan runduna ta 301 Field Artillery Regiment Gombe, Kanal Musa Ahmed, tare da tsohon kwamanda, Kanal Abu Ndah.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tinubu, NLC da TUC Sun Shiga Ganawar Gaggawa Kan Wani Batu
Wakilinmu ya rawaito cewa, gwamnan ya yi wa sabon kwamandan maraba a hukumance, inda ya ba shi tabbacin goyon bayan da gwamnatin jihar ta saba baiwa rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro a aikin yaki da kalubalen tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Gombe.
Sannan ya yi amfani da wannan dama wajen yabawa runduna ta 301 Field Artillery Regiment Gombe bisa rawar da take takawa wajen karfafa harkar tsaro a jihar da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.
“Ina so in yaba wa rundunar sojojin Najeriya gaba daya saboda tabbatar da kwarewa a bakin aiki, wannan gwamnati za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kulla kyakkyawar alaka da su wajen yaki da miyagun laifuka,” in ji Yahaya.
Gwamnan ya yabawa tsohon kwamandan, Kanal Ndah, bisa ayyukan da yake yi a jihar Gombe, da kuma bayar da gudunmawa sosai wajen tabbatar da tsaro a lokacin da yake aiki, tare da yi masa fatan samun nasara a wannan sabon aikin da aka bashi.
A nasa bangaren, sabon kwamandan runduna ta 301 Artillery Regiment, Kanal Ahmed, ya bukaci da a ci gaba da ba gwamnati da jama’ar jihar Gombe goyon baya da hadin kai ga rundunar sojojin Nijeriya, kasancewar wani bangare ne na gine-ginen tsaro a jihar domin samun damar cimma nasara a aikinsu na kasa.
Kazalika ya kuma bukaci jama’a da su yi aiki tare da gwamnatin jiha da ’yan uwa hukumomin tsaro wajen wanzar da zaman lafiya da doka da oda.
Har ila yau, tsohon kwamandan, Kanal Ndah, ya gode wa Gwamna Yahaya, bisa goyon bayan da yake bai wa runduna ta 301 na Artillery da kuma sojojin Nijeriya da ma sauran jami’an tsaro; kuma musamman saboda jajircewarsa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
A wani labarin kuma, Borno: Fitacciyar Kungiyar Marlian Ta Shiga Ha’ula’i, Gwamna Zulum Ya Bada Wani Umarni
Gwamnan Borno Babagana Zulum ya umurci jami’an tsaro da su murkushe ’yan kungiyar Marlian da ake kyautata zaton suna addabar jama’a a wasu sassan Maiduguri da Jere da ke cikin birnin jhar.
Kungiyar ta Marlian wadda wasu matasa ke da alaka da shaye-shayen miyagun kwayoyi, ta yi kaurin suna wajen aikata laifuka da dama da suka hada da karbar kudi, fashi da makami, da safarar miyagun kwayoyi, da ayyukan ta’addanci da suka hada da kashe jami’an tsaro.