Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa Farfesa Rufai Alkali ya bayyana farin cikin sa da samun rabauta da masu sauyin sheka da jam’iyyar ke ci gaba da yi.
Farfesa Alkali ya kuma bayyana jin dadinsa, kan komawar Sanatan Kano ta tsakiya Ibrahim Shekarau cikin jam’iyyar daga jam’iyyar APC.
Komawar Shekarau na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Abdulmumin Kofa Daraktan yakin neman zaben Bola Tinubu ya koma cikin jam’iyyar.
Dangane da zaben 2023, Farfesa Alkali ya ce suna fatan zasu bayar da mamaki a zaben, domin kuwa yanzu haka jam’iyyar su itace ke tashe ta hanyar ci gaba da samun magoya baya.
A don haka ne, jam’iyyar ta sanar da dage ranar zaben fidda gwani na yan takarar Gwamnan, da kuma Sanata.
Sakataren Jam’iyyar NNPP, kuma shugaban kwamitin shirya taron jam’iyyar na kasa Dipo Olayoku, shine ya sanar da hakan cikin wata Sanarwa da ya rabata ga manema labarai.