Wani matashi da ake kyautata zaton dan shekara 17 ne, mai suna Abdulkadir, ya nutse a cikin teku yayin da yake ninkaya a jihar Kwara.
Lamarin dai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a ranar Asabar, ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Alhamis a kauyen Ora da ke Monasara a karamar hukumar Ifelodun dake jihar inda matashin yake tekun bayan ya dawo daga makarantar da ya rubuta jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) da ke gudana.
A cewar wata majiya daga kauyen, “Abdulkabir ya roki daya daga cikin mazauna unguwar mai suna Tosho mai shekaru 10 da abokinsa da su kai shi rafi don yin iyo.
“A kan hanyarsu ta zuwa ne suka hadu da daya daga cikin malaman makarantar wanda ya tambayi inda za su, sai suka yi masa karya cewa za su sayi biredi. Amma a karshe ya mutu a cikin tekun kuma an gano gawarsa,” kamar yadda majiyar ta ce.
Rahotanni sun nuna cewa mahaifinsa, Mista Abdulsalam, wanda ke zaune a unguwar Idi-Ape a Ilorin, ya amince a binne shi a gefen bakin kogi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi (SP), da aka tuntube shi ya ce ba a yi masa bayani ba kan faruwar lamarin.