Shugaban kasar Sudan Mista Salva Kiir ya ƙi amincewa a gudanar da taron rantsar da sabbin yan majalisun kasar ranar Juma’a.
Kamar yadda aka fadi tun farko, an tsara rantsar da yan majalisun jihohi da na tarayya ne da aka sauya fasalinsu a ranar juma’a, to amma Mista Kiir ya ɗage har zuwa ranar Litinin.
Dalilin ɗage rantsuwar dai kamar yadda aka ayyana shine don girmama ranar Martyrs, ranar dake zama na Jimamin mutuwar gwarzon da ya yi gwagwarmayar kafa kasar wanda ya mutu ne a shekarar 2005 sakamakon hatsarin Jirgi mai saukar ungulu.
Kazalaika a ranar ne ake bikin tunawa da sauran yan mazan jiya da suka yi gwagwarmayar kwarto wa Sudan ta Kudu ƴancinta.
Kuma tuni Mista Salva Kiir ya umarci yan kasar da kowa ya zauna a gida don tunawa da wadannan mazajen jiya.