By Abbas Yakubu Yaura
Shugabannin al’umma a Jimeta sun yi watsi da shawarar samar da karin wasu gundumomin yaki guda biyu a cikin garin Adamawa.
Tawagar tasu mai girma karkashin jagorancin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa Muhammad Turaki, a ranar Larabar da ta gabata, sun mika matsayarsu ga kwamitin wucin gadi na majalisar kan samar da karin gundumomi a Yola.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Turaki ya yi nuni da cewa, samar da sabbin gundumomi bai dace ba ta fuskar tattalin arziki duba da yadda wasu gundumomin da ake dasu ba zasu iya biyan albashi na wasu watanni ba.
A nasa jawabin, Usman Wakili, tsohon mai baiwa tsohon Gwamna Murtala Nyako shawara kan harkokin siyasa, ya ce matakin bai samu goyon bayan mafi yawan al’ummar Jimeta ba.
A nasa martanin shugaban kwamitin Hammantukur Yettisuri wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar ya tabbatarwa da shugabannin al’umma cewa majalisar za ta yi adalci kan abubuwan da suka gabatar tare da yin la’akari da dalilansu.
Sai dai ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta da hannu a yunkurin samar da sabbin gundumomi.