By Abbas Yakubu Yaura
Iyalan Alexander Uzoma sun yi kira da a yi adalci kan kisan da wasu da ake zargin masu damfara ta yanar gizo ne, wadanda aka fi sani da Yahoo-boys suka kashe dan uwansu a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, a makon daya gabata, ya ce jami’an rundunar ‘yan sandan Ogun sun kama wasu matasa hudu, wadanda suka yi ikirarin cewa sun jefar da gawar Alexander dan shekara 20 a kan gadar Kuto dake Abeokuta a ranar 20 ga watan Nuwamba.
A cewar wata sanarwa da Oyeyemi ya fitar, wadanda ake zargin sun ce Alexander, dalibi mai mataki karatu na 300 a Jami’ar Jihar Imo, ya ziyarce su ne domin koyon zamba ta yanar gizo wato Intanet, inda ya dauki wani abu mai suna Colorado kuma ake zargin ya mutu.
Sai dai ’yan uwan dalibin sun musanta cewa sun shaida wa ’yan sanda cewa dan uwansu ya fita ne don ganin abokinsa, inda suka ce ya bar gida ne don zuwa kallon wasan kwallon kafa a wata cibiyar kallo da ke kusa da Adigbe, Abeokuta, kasancewarsa masoyin Manchester United ne.
Daya daga cikin ‘yan uwan mai suna Jude Uzoma, ya shaida wa manema labarai cewa bai iya gane yadda ‘yan sandan suka zo wajen shaida wa jama’a cewa dan uwansa ya je ganin abokansa.
“Ni ne na rubuta sanarwar lokacin da muka isa ofishin ‘yan sanda na Adigbe. Ba mu gaya musu cewa ya je ya ga wani abokinsa ba.Mu munce musu ne ya je kallon kwallon kafa. Daga ina ’yan sanda suka samo wannan bayanin?” Jude ya tambaya.
Ya bayyana yadda shi da mahaifiyarsa suka ziyarci Ibara, Obada, Lafenwa da ofisoshin ‘yan sanda kusan 15, ciki har da hedkwatar ‘yan sandan jihar, Eleweran, wajen neman yaron da ya bata, wanda ya ce wayarsa ta yi ta ringing ba tare da an amsa ba.
Bayan da aka kasa kokarin gano Alexander a cikin kwanaki biyu, Jude ya ce an sanar da kungiyar ‘yan asalin Imo dake Abeokuta, inda ya ce kokarin da kungiyar ta yi ya sa aka mika karar zuwa hedikwatar ‘yan sanda.
Haka kuma, babban yayan marigayin, Augustine Uzoma, ya ce ‘yan sanda sun sanar da su cewa dan uwansa marigayi yana hulda da daya daga cikin ‘yan Yahoo-boy, wanda ya kira shi ta waya.
“Ya yi mu’amala da daya ne kawai daga cikinsu; ba mu san yadda sauran ukun suka shigo cikin hoton ba. Kamar yadda wadanda ake zargin suka shaida wa ‘yan sanda, sun ce ya bi su har gidan su; suka ci abinci, suka dauki Colorado, suka yi barci suka farka wajen karfe 8 na dare. Da suka farka sai suka ga ya yi amai a jikinsa ya mutu.