Shugabar Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya UN GA María Fernanda Espinosa Garcés za ta ziyarci fadar shugaban Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja a yau Talata don ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.
Wakilinmu ya bayyana cewa, Shugabar ta isa fadar shugaban kasar da misalin karfe 11:40 na safe. Ana saran Ministoci da manyan jami’an gwamnatin Najeriya za su halarci ganawar da za a yi tare da shugaba Buhari.