Daga: Abbas Yakubu Yaura
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa a majalisar tarayya, Honorabul Shina Abiola Peller, ya fice daga jam’iyyar APC.
Peller wanda dan asalin garin Iseyin ne a shiyyar Oke Ogun geo-political zone a jihar Oyo, ya bayyana hakan ne ta wata wasika da ya aikewa shugaban gundumar sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Guguwar Iska Ta Kashe Wani Yaro Dan Shekara 7, Ta Raunata Wasu Bakwai A Jihar Jigawa
Wakilinmu ya tuna cewa an zabi Peller ne a jam’iyyar APC a shekarar 2019.
Ya kasance daya daga cikin masu neman kujerar Sanatan Oyo ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a zaben fidda gwanin da aka yi kwanan nan.
Sai dai dan majalisar ya fice daga jam’iyyar ta APC.
Peller, a cikin wasikar da ya sanya wa hannu da kansa kuma ya aika wa shugaban jam’iyyar APC na mazabar sa ta a kwati na 9 dake Koso a karamar hukumar Iseyin, ya dage cewa ya dauki matakin ne bayan ya yi shawarwari da jama’ar sa.
Dan majalisar ya ce rashin bin tsarin dimokuradiyyar da wasu jiga-jigan jam’iyyar ke yi musamman a jihar Oyo ya nuna cewa jama’a tun daga tushe da matasa za su ci gaba da kasancewa cikin jin kai ga wasu tsiraru a sama.
Ya yi zargin cewa wasu mutane a cikin jam’iyyar ne suka dora dan takarar da suke so ba tare da bukatar jama’a ba.
Ya ci gaba da cewa ya fice daga jam’iyyar APC ne saboda jama’ar sa sun nemi ya yi hakan.
Sannan ya bayyana cewa ya yanke shawarar shiga siyasa ne ba don son rai ba, illa muradin matasan Najeriya baki daya da mutanen Oke Ogun.
Ya ce, “Na rubuto ne domin in sanar da ku ficewar da na yi daga jam’iyyar APC.
“Na dauki wannan matakin ne bayan shawarwarin da na yi da jama’ata daga yankin Oke Ogun da ma wadanda suke ganin an wulakanta su saboda rashin bin tsarin dimokaradiyya da yanke shawarar wasu ‘yan jam’iyyar APC na jihar Oyo.
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa’azi daga kasa zuwa sama a karkashin jam’iyyar APC, amma rashin tsarin dimokradiyya na wasu jiga-jigan jam’iyyar musamman a jihar Oyo ya nuna cewa jama’a tun daga tushe da kuma matasa za su ci gaba da kasancewa cikin tausayin ‘yan tsiraru a sama. , wadanda suke dora dan takarar da suke so ba tare da son jama’a ba, kamar yadda a kwanan nan suka shaida a gundumar Oyo ta Arewa da nake zaune.
Don haka al’ummata sun yanke shawarar cewa mu janye daga jam’iyyarmu ta APC, kuma na yi tarayya da su gaba daya domin na tsunduma cikin harkokin siyasa ba don son rai ba, illa muradin matasan Najeriya da mutanen Oke Ogun.Don haka na bar jam’iyyar APC”.
Comments 1