Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kame wasu mayakan Boko Haram 16 a yankin Pulka dake karamar hukumar Gwoza.
Dakarun Nujeriyar sun kai samamen ne a ranar 20 ga watan Oktoban 2019, inda suka kame mayakan, ciki har da wasu manyan kwamandojin kungiyar ta Boko Haram da ke cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo.
Mai magana da yawun sojojin Nijeriya Kanal Aminu Iliyasu, ya ce kwamandojin masu tada kayar bayan da suka shiga hannu sun hada da Lawan Abubakar Garliga, mutum na 41 da kuma Bayaga Manye na 90, dukkaninsu da ke cikin manyan jagororin kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.
Kakakin sojin Nijeriyar Kanal Iliyasu, ya ce binciken farko da suka gudanar, ya nuna cewa, wasu daga cikin mayakan da suka kama, na cikin wadanda suka kai kazaman hare-hare a Pulka da Gwoza, sai kuma yiwa wasu jami’an ‘yan sanda kisan gilla a shekarun baya.