Sojojin Najeriya biyu sun mutu a ranar Lahadin da ta gabata yayin da sojoji ke fafatawa da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP a karamar hukumar Gajiram Nganzai ta jihar Borno.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu ya ce ‘yan ta’addan sun samu karin asarar rayuka yayin da sojojin Operation Hadin Kai (OPHK) suka farmasu.
Nwachukwu ya ce jami’an rundunar sojin Sam Dana kasa dake rundunar Operation Hadin Kai OPHK tare da dakarun sashe na 3, sun farmaki ‘yan ta’addan da suka yi yunkurin kutsawa cikin wani sansanin soji, ta hanyar amfani da manyan bindigogi da wasu Tankokin yaki.
Ya ce ‘yan ta’addan sun ja da baya cikin rudani, inda suka rasa wasu daga cikin su da kuma yin asarar kayan aikin su.
A cewarsa, sojojin sun kwato bindigu kirar AK 47 guda 10, Bindigogin Anti-Aircraft guda daya, da alburusai 61 na Malamin PKT da dai sauransu.
“Wasu gawawwakin ‘yan ta’addan da aka kone Amma Abin baƙin ciki shine, ƙwararrun sojojin Najeriya biyu sun rasa rayukan su.
“Shugaban hafsan soji, Lt.-Gen. Faruk Yahaya, ya bukaci sojojin da su ci gaba da gudanar da ayyukansu, har sai an kawar da ragowar ‘yan ta’addan da ke yin Kaura zuwa wasu yankuna na kasar nan.” Inji shi.