Jami’an runduna ta 81 na rundunar Sojojin kasa ta Najeriya sun samu nasarar cafke wasu mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram yayin da suke tsaka da kitsa yadda zasu kaddamar da wasu hare hare a jihar Leags.
Jaridar The Nation ta ruwaito rundunar Sojan ce ta sanar da haka a ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba ta bakin babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Olu Irefin, wanda yace tuni sun garzaya da yan ta’addan zuwa babbar birnin tarayya Abuja.
Bayanai sun ce ‘yan ta’addan sun yi kokarin kaddamar da hare hare ne a wata Jami’a dake garin Legas a makonni biyu da suka gabata, amma aka yi sa’a Sojoji suka dakile yunkurin yan ta’addan, inda ta kama mutane 4 dake da hannu cikin shirin, sa’annan aka kama sauran daga bisani, dukkaninsu sun tabbatar da kasancewa a kungiyar Boko Haram.