Sama da ƴan bindiga da ƴan ta’adda Sojojin Najeriya suka kashe a faɗin jahohin Arewa, a tsakanin 15 ga watan Oktoba da 28 na wannan watan na shekarar 2021.
Bayanai sun nuna cewa sama da ƴan ta’adda 118 aka kashe, a yayinda ƴan bindiga 71 sojoji suka kashe a yaƙin da suka kai a lokacin da aka ambata.
Haka zalika, a lokacin da aka ambata, an kama ƴan bindiga 50, a yayinda aka ceto mutane 27 da akayi garkuwa dasu.

KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Ministan Sufuri, Ibrahim Bio ya canja sheƙa daga APC zuwa PDP
Dayake jawabi ga Manema labaru akan yaƙin da sojoji suka yi a cikin sati biyu a ranar Alhamis a Abuja, muƙaddashin Daraktan Harkokin Kafafen Yaɗa Labaru na Soji Benard Onyeuko, ya bayyana cewa kimanin ƴan ta’adda dubu 1,199 da iyalan su, da suka ƙunshi maza 114 da mata 312, gami da yara 773 suka mika wuya ga Sojoji.
A jawabin daya taɓa yi, yace kimanin ƴan ta’adda dubu 13,243 suka miƙa wuya, wanda yanzu adadin waɗanda suka miƙa wuya yakai dubu 14,442.
Onyeuko yace “a lokacin gudanar da yaƙin a dai-dai lokacin, kimanin ƴan ta’adda 38 akan kashe ciki harda sabon shugaban ISWAP, Baƙo.
An kuma kama ƴan ta’adda 11 da masu basu bayanan sirri a lokacin gudanar da yaƙin.