By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar sojin Najeriya ta karyata zargin da ake da hannun sojoji a wani fafatawar da suka yi da bindiga, sakamakon rashin jituwar da ta barke a kauyen Magama da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar, Janar Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya bayyana rahoton da kafafen yada labarai suka wallafa a matsayin mara tushe, rashin gaskiya kuma kawai tunanin marubucin, da nufin bata sunan rundunar.
Sannan ya ce babu wani soja da ya rasa ransa ko kuma ya shiga wata arangama da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a garin Magama kamar yadda aka ruwaito.
“Sabanin zage-zage da kafafen yada labarai na yanar gizo ke yi, sojojin Najeriya da aka tura yankin Arewa maso Yamma sun jajirce wajen yaki da ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka da ke addabar yankin.
“Ba a ba su izinin shiga kowane nau’i na hakar ma’adinai ba, ko na halal ne ko na haram.
Comments 1