Sojoji sun yi nasarar hallaka Ƴan bindiga uku Tare Da kwace Muggan Makamai a Taraba
Dakarun runduna ta 6 ta Sojojin Najeriya dake Jalingo babban Birnin Jihar Taraba sun kashe wasu ‘yan bindiga uku tare da kwato Makamai da alburusai a maɓoyarsu.
Wannan farmaki na musamman wanda ya gudana a kauyen Chibi dake ƙaramar Hukumar Karim Lamido, an ce an samu nasarar ne bayan wani rahoton sirri da aka samu.
Matakin da Sojojin suka ɗauka cikin gaggawa a cewar Kwamandan Rundunar Birgediya Janar Kingsley Uwa ya kai ga kawar da masu laifin tare da kwato wasu muhimman makamai masu hatsari.
KARANTA NAN:An Bai Wa Iyalan Jami’an da Suka Mutu Cekin N41m a Jigawa
Daga cikin kayayyakin da aka kama akwai bindigogi kirar AK 47 guda biyu, da babur ɗin da ’yan ta’addan ke amfani da su da kuma wata buta mai ɗauke da harsashi guda 40 ƙirar 7.62 MM wanda shima alburusai ne na musamman.
Da yake yabawa sojojin bisa jajircewarsu da kuma yadda suke gudanar da aikin, ya jaddada ƙudirin rundunar na kawar da masu aikata laifuka a Jihar Taraba, ya kuma baiwa mazauna Jihar tabbacin ci gaba da kokarin wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
A wani labarin kuma:Hukumar kashe gobara ta ceto wani mutum da yayi yunƙurin aikata kisan Kai kan cinikin bizar N2m a Kano
Hukumar kashe gobara ta ceto wani mutum daga yunƙurin aikata kisan Kai kan cinikin bizar N2m a Kano
Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano a ranar Alhamis ta ce ta ceto wani Mutum mai suna Saifillahi Rabiu dan shekara 37 da ake zargi da yunkurin kashe kansa kan wata yarjejeniya da ta kasa cimma ruwa.
Jami’in hulɗa da Jama’a na Hukumar kashe gobara Alhaji Saminu Abdullahi ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano.
Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis a Titin Jihar ta ƙaramar Hukumar Tarauni dake Jihar Kano.
A cewar sa, Mun samu kiran waya da misalin ƙarfe 10:07 na safe daga ma’aikatar ayyuka da gidaje ta Jihar Kano kan yunkurin kashe kansa ta hanyar rataya akan wata bishiya.
Da samun labarin mun aika da motar kashe gobara zuwa wurin da misalin karfe 10:10 na safe,” inji shi