Hukumar kashe gobara ta ceto wani mutum da yayi yunƙurin aikata kisan Kai kan cinikin bizar N2m a Kano
Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano a ranar Alhamis ta ce ta ceto wani Mutum mai suna Saifillahi Rabiu dan shekara 37 da ake zargi da yunkurin kashe kansa kan wata yarjejeniya da ta kasa cimma ruwa.
Jami’in hulɗa da Jama’a na Hukumar kashe gobara Alhaji Saminu Abdullahi ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano.
Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis a Titin Jihar ta ƙaramar Hukumar Tarauni dake Jihar Kano.
A cewar sa, Mun samu kiran waya da misalin ƙarfe 10:07 na safe daga ma’aikatar ayyuka da gidaje ta Jihar Kano kan yunkurin kashe kansa ta hanyar rataya akan wata bishiya.
KARANTA NAN:An Bai Wa Iyalan Jami’an da Suka Mutu Cekin N41m a Jigawa
Da samun labarin mun aika da motar kashe gobara zuwa wurin da misalin karfe 10:10 na safe,” inji shi
A cewar sanarwar, Rabiu wani mazaunin Semegu Quarters ne da ya yi yunkurin rataye kansa kan rashin mayar da kuɗi Naira miliyan 2 ga waɗanda ya yi ƙoƙarin shige masu gaba wajen samun bizar tafiya ƙasar waje.
A yayin da muke tambayoyi da gudanar da bincike, mun tattaro cewa Rabiu ya haɗa wasu mutane da masu gudanar da bizar tafiye-tafiye zuwa kasashen waje wanda hakan ya yi nasarar kammaluwa, sai dai waɗanda ya yi ƙoƙarin taimakawa duk da haka suka ki amincewa da bizar ɗin, inda su ka ce ba irin ta suka nema ba, sai suka bukaci da ya mayar musu da kudadensu da suka biya, cewa sun fasa.
Mun tattaro cewa yayi ƙoƙari har ya tara rabin kuɗin wato Naira Miliyan ɗaya, amma matsin lamba da barazana daga mutanen ne ya sa ya yi kokarin kashe kansa,” in ji PRO.
Ya kuma bayyana cewa an ceto Rabiu da ransa aka mika shi ga sashin ‘yan sanda domin kara fadada bincike.
A wani labarin kuma:Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tsare Mutane Biyar Masu Biyayya Ga Gwamnan Ribas Fubara
Kotu ta yanke wa wasu ‘yan banga biyar hukuncin kisa a Kano
A ranar Alhamis ne wata babbar kotu a Jihar Kano ta yanke wa wasu ‘yan kungiyar ‘yan banga biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutuwar wani yaro dan shekara 17.
Mutum biyar da aka yankewa hukuncin dai sun hada da Emmanuel……….