Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke Zamfara a ranar Litinin ta tabbatar da ceto dalibai 13 da wasu mutane uku da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar 12 ga watan Satumba,Jami’ar ta tabbatar da ci gaban ta hanyar ingantaccen shafin ta na twitter.
A wani lamari mai ban mamaki da ya faru, mutane 16, dalibai 13 da kuma leburori uku sun sami ‘yancinsu, saboda jajircewar da sojoji suka yi.
Muna kuma mika godiyarmu ga Ubangiji Madaukakin Sarki da ya ba su karfin gwiwa da juriyar jure wa wannan mawuyacin hali.
Karanta nanZamu Magance Wahalhalun Da Ake Sha Wajen Samun Fasfo A Najeriya-Minista
Ayyukan ceto, wanda jami’an soji da suka sadaukar da kansu suka gudanar, ya nuna jajircewarsu wajen kare lafiya da tsaron ‘yan kasarmu in ji shi.
Daliban matan an sace su ne daga gidajen da suke haya a Sabon-Gida mai tazarar mita 200 daga harabar jami’ar.
Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu ma’aikatan ginin wani kamfani mai suna GUPRAN Engineering Services Ltd da suke gudanar da wani aiki a jami’ar.
A jiya ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su kubutar da sauran dalibai mata na jami’ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara, wadanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su kwanan nan.
Tinubu ya lura cewa babu wani dalili na ɗabi’a ga irin waɗannan munanan laifuka akan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba waɗanda “laifi” kawai shine neman ilimi mai inganci.
Sai dai da yake bayanin yadda aka ‘yanto daliban bakwai, Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, ya ce an kubutar da daliban bakwai ne tare da wasu maza uku ma’aikatan Gupran Engineering Services Ltd.
A wani labarin kumaSai A Karshen Wannan Shekarar Zamu Janye Sojojinmu Daga Kasar Nijar-Macron
Ga sunayen daliban da aka ‘yanta a kasa
1. Rukayya Sani Batola
2. Merry Monday
3. Maryam Salawuddeen
4. Salamatu Jummai Dahiru
5. Fiddausi Abdulazeez
6. Amamatullahi Asabe Dahiru
7. Ketura Bulus
8. Felicia Lahadi
9. Jamila Ahmad
10. Aisha Aminu Ujong
11. Mariya Abdulrahman Usman
12. Usaina Abdulrahman
13. Saadatu Aminu Abubakar