Gwamnatin tarayya ta fara yin garambawul domin kawar da cikas ga harkar bayar da fasfo da karbar fasfo din Najeriya.
Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a karshen mako yayin da ya karbi bakuncin jakadan kungiyar tarayyar turai a Najeriya, Samuela Isopi a Abuja.
Tunji-Ojo ya bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa fasfo din Najeriya ya dawo da martabarsa ta hanyar rage satar mutane.
Karanta nanSai A Karshen Wannan Shekarar Zamu Janye Sojojinmu Daga Kasar Nijar-Macron
A cewarsa, ana shirin rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya da kashi 40 cikin 100 ta hanyoyin da ba sai an wahala ba.
Ya yi kira ga EU da ta taimakawa nahiyar ta kawo karshen kalubalen da ta ke fuskanta da suka hada da safarar mutane dafa nahiyar Afirika zuwa galibin wasu kasashen turawa.
Ya ce mun fara aikin ne domin warware matsalolin da ke tattare da aikace-aikacen fasfo na kasa da kasa. A yau, mun sami ci gaba mai yawa. Muna kuma aiki kan hanyoyin rage satar bayanan sirri. Muna so mu tabbatar da koren fasfo ya dawo da kima da mutuncinsa.
Idan za mu iya magance laifuka da matsalolin ƙaura a Najeriya, Afirka za ta fi dacewa da ita.”
A nata bangaren, Isop ta yi alkawarin bayar da goyon bayan kungiyar EU ta hanyar sarrafa fasaha na yin hijira ba bisa ka’ida ba, fataucin mutane da fasa kwauri.
Inda ta bayyana cewar zata yi iyakar kokarinta wajen ganin an samu ragowar kwararar mutane daga Afirika zuwa kasashen turai ba bisa ka’ida da bin doka ba.
A wani labarin kuma
Ba Da Sani Na Gwamnatin Tarayya Ke Sulhu Da yan Bindiga Ba-Gwamnan Jahar Zamfara
Gwamnatin jahar Zamfara a karkashin jagorancin Gwamna Dr Daud Lawal Dare ta bayyana cewar ba da umarninta ko da saninta ake cigaba da tattaunawar sulhu da ta ce gwamnatin tarayya ke daukar nauyi ba