Manyan shugabannin ‘yan ta’adda da sojin sama suka kashe sun hada da Abu Asad, Ibrahim Nakeeb, Mujaheed Dimtu, Mustafa Munzir da mayaka sama da 100 a harin da sojojin saman Najeriya suka kai musu a Tagoshe dake tsaunin Mandara a jihar Borno.
Daraktan hulda da jama’a da yada labarai (DOPRI) a cikin wata sanarwa ya ce harin da aka kai a ranar 24 ga watan Nuwamban 2023 ya kuma lalata gine-ginen ‘yan ta’addan da dakaru.
Karanta nan‘Yan Nijeriya Na Gab Da Samun Wutar Nepa Awa 24-Ministan Wutar Lantarki
Ya ce an ga ‘yan ta’addan suna ta taruwa a wani waje da ke dauke da wasu gine-ginen da aka dankare da su a cikin itatuwa da dama.
Air Commodore Gabkwet ya ce ‘yan ta’addan na taruwa a wurin domin yin wani shiri mai kyau ko kuma suna shirin kai wani babban hari kan dakarunmu.
Ya ci gaba da cewa,sama da ‘yan ta’adda 100 dauke da muggan makamai an gansu suna ta harbin bindiga tare da zagayawa cikin daji.
Akwai kuma alamun Abu Asad, jigo a kungiyar Ali Ngulde a karkashin Boko Haram, da kuma sauran ‘yan ta’adda kamar Ibrahim Nakeeb, Mujaheed Dimtu, Mustafa Munzir da mayaka da dama na daga cikin ‘yan ta’addan da aka kawar da su a harin ta sama inji shi.
A wani labarin kumaEmiefiele Ya Lalata CBN Kafin Ya Barta-Gwamnan CBN Cardoso
Shugaban Rundunar Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya yabawa Kwamandan Rundunar Sojojin Sama da mutanensa, ya kuma bukace su da su ci gaba da hada hannu da rundunar ta kasa yayin da suke ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Dole ne mu ci gaba da tabbatar da amanar da Gwamnatin Tarayya da al’ummarmu suka ba mu ta hanyar tabbatar da cewa mun yi duk mai yiwuwa wajen ganin wadannan ‘yan ta’adda sun mika wuya ko kuma a kawar da su gaba daya.