A ranar Juma’ar da ta gabata ne ‘yan ta’adda a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara sun yi garkuwa da mutane sama da 100 a wasu hare-hare daban-daban da suka kai a kauyuka da dama saboda gaza biyan harajin kariya na Naira miliyan 110.
Ana kyautata zaton ‘yan ta’addan da suka kai harin suna biyayya ga wani sarkin ‘yan ta’adda mai suna Damina, wanda ke aiki a kewayen Dansadau na jihar.
Karanta nanSojojin Nijeriya Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Fiye Da 100 A Wani Harin Sama A Jahar Borno
PREMIUM TIMES ta tattaro cewa wadanda aka sace sun fito ne daga Mutunji, Unguwar Kawo, Kwantar Dutsi da Sabon Garin Mahuta.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa BBC Hausa cewa Mista Damina ya jagoranci gungun ‘yan ta’adda a kan babura inda suka kewaye al’ummar ‘yan mintuna bayan sallar magariba da karfe 8:00 na dare.
Muna zaune a wani wuri da ake kira ‘Yar Kasuwa bayan Sallar Isha’i, sai ‘yan ta’addan suka far wa al’umma. Sun kewaye al’umma yayin da wasu suka shiga cikin gidaje sun daidaita mutane cikin daji inji shi.
Yace daga cikin wadanda ‘yan bindigar suka sace akwai mata da kananan yara wadanda basu jiba basu gani ba.
A wani labarin kumaKorarren Sufeton ‘Yan Sanda Ya Gurfana Gaban Kotu Akan Sayar Da Bindigar Hukuma
Mutanen garin Mutunji ba su sani ba, an kai farmakin a lokacin da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su.
Sun kuma kai hari ga wasu al’ummomi da suka hada da Unguwar Kawo, Kwanar Dutsi da Sabon Garin Mahuta tare da kwashe mutane da dama. Mun samu aƙalla mutane 100. Har yanzu muna kirgawa don gano ainihin adadin wadanda aka kama, ”in ji majiyar.