Tun bayan juyin mulkin da babban hafsan Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya jagoranta, ya dakatar da shirin raba madafun iko tsakanin sojoji da fararen hula da aka amince dasu bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a shekara ta 2019 da nufin kai ga gudanar da zaben dimokuradiyya a karshen shekara ta 2023.
An tsare manyan fararen hula da suka hada da ministoci da dama, sannan an tsare firaminista Abdalla Hamdok a gidan kaso.
Saidai Tun daga wannan lokaci, yunkurin shiga tsakani daya shafi Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a sako fursunonin da kuma komawa kan karagar mulki sai dai wata majiya daga hambararriyar gwamnatin tace yunkurin ya ci tura.
Kazalika jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Rahotannin baya-bayan nan na cewa kusan malamai 100 ne sojoji suka kama awani bangare na cigaba da muzgunawa fararen hula a kasar.
Comments 2