Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na III, ya ba da tabbacin bayar da cikakken goyon baya ga Hukumar USAID Breakthrough Action Nigeria da sauran hukumomin bayar da agaji da ke aiwatar da shirye-shirye daban-daban a jihar Sokoto.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Ya bayar da wannan tabbacin ne a Sokoto ranar Juma’a a lokacin da tawagar USAID Partners Forum karkashin jagorancin Breakthrough Action suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa.
Ya ce yana sane da irin tallafin da hukumar ta USAID ke yi a sassa daban-daban da suka hada da ilimi, lafiya, muhalli, noma, karfafa kasuwanci da sauran su a Sokoto da sauran su.
KU KARANTA KUMA Sultan Ya Bayyana Yadda Za A Kaucewa Tashin Hankali A Zaben 2023
Sarkin ya ce tallafin ya kara habaka rayuwar ‘yan kasa tare da mayar da hankali kan manufofin gwamnati wajen samar da ingantaccen amfani da kuma kula da albarkatun ruwa a cikin al’umma.
Ya kuma ba da tabbacin cewa Majalisar Sarkin Musulmi za ta ci gaba da hada gwiwa da hukumomi domin cin gajiyar shirye-shiryen da ayyukan.
Tun da farko, shugaban tawagar, Dr Abdulrahman Ibrahim, kuma Ko’odinetan kungiyar Breakthrough Action Nigeria, ya ce
tawagar ta kasance a fadar Sarkin Musulmi domin neman albarka tare da sanar da shi shirye-shirye daban-daban da Hukumar USAID ke aiwatarwa a jihar Sokoto.
Ibrahim ya ce sun kai ziyarar ne domin neman goyon bayan Sarkin Musulmi ga shirye-shiryen da Hukumar USAID ke tallafawa.
A cewarsa, tawagar tana shirin tantancewa da mayar hankali kan abinci mai gina jiki da nufin inganta tsare-tsaren aiwatar da karin kudade don samar da abinci mai gina jiki don samun wadatar abinci.
Ibrahim ya yi kira da a kara saka hannun jari masu zaman kansu a ci gaba da yin rijistar tsarin inshorar lafiya da gwamnatin jihar Sokoto ke aiwatarwa bisa la’akari da muhimmancinsa wajen samun nasarar samar da kiwon lafiya.
Kamfanin dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa abokan hadin gwiwar da suka halarci taron sun hada da Integrated Health Project (IHP), GHSC-PSM, Health Workforce, KP Care 2 Project, MCGL, State2State da USAID Advancing Nutrition. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Keyamo Ya Maka EFCC, ICPC, CCB A Kotu, Kan Bukatar Da Yayi Musu Na Su Kama Atiku
Karamin Ministan Kwadago da Aikin yi Festus Keyamo ya maka hukumar ICPC da EFCC da kuma CCB a gaban kuliya bisa rashin kamawa, yi masa tambayoyi da kuma gurfanar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar bisa zarginsa da satar dukiyar al’umma.
Keyamo ya koma Atiku ne a karar da aka shigar ranar 20 ga watan Janairun 2023.