Kocin Manchester United, Erik ten Hag, ya ce kungiyarsa za ta yi duk abin da za ta yi don sake doke Arsenal.
Red Devils ita ce kungiya daya tilo da ta samu maki uku a ragar Mikel Arteta a wannan kakar.
United ta ci 3-1 a fafatawar da suka yi a Old Trafford a watan Satumba.
KU KARANTA: Hukumar Kwastam Tayi Nadin Muƙaman Maye Gurbin Manyan Jami’ai 20
Amma Ten Hag ya yarda cewa Gunners sun inganta tun lokacin kuma za su kasance abokan hamayya masu wahala wuyar sha’ani.
“Suna kan gudu mai kyau kuma ya rage namu mu doke wannan hazaka ta su, kuma za mu yi duk abin da za mu yi wajen nasara akan su.”
Ten Hag ya fadawa taron manema labarai a ranar Juma’a.
A wani labarin kuma: Keyamo Ya Maka EFCC, ICPC, CCB A Kotu, Kan Bukatar Da Yayi Musu Na Su Kama Atiku
Karamin Ministan Kwadago da Aikin yi Festus Keyamo ya maka hukumar ICPC da EFCC da kuma CCB a gaban kuliya bisa rashin kamawa, yi masa tambayoyi da kuma gurfanar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar bisa zarginsa da satar dukiyar al’umma.
Keyamo ya koma Atiku ne a karar da aka shigar ranar 20 ga watan Janairun 2023.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Litinin din da ta gabata ne mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kai karar shugabannin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, da hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) da kuma Code of Conduct Bureau (CCB), inda ya zarge su kan Dan takarar PDP na manyan laifuka hudu.