Wasu matasan barayi sun shiga cakwakiya bayan sun yi yunkurin yin fashi a wani gida cikin kwanakin karshen mako, Dailymail ta ruwaito.
Sai dai bayan shiga sai suka gane cewa gidan kwararren dan dambe, Casey Caswell suma shiga.
KU KARANTA: Wata babbar kotun Ekiti ta ɗaure wata mata bisa satar kayan Naira Miliyan 5
Fitaccen dan kwallon asalin daga Buckinghamshire yake Birtaniya, kuma yana da tarihin buge mutane 7 yayin da ba a taba matar da shi ba.
Bayan kamarorin tsaronsa suka bayyana masa cewa akwai mutane, wanda nan da nan wayarsa ta fara ruri.
Nan da nan ya bayyana a kofar gaba inda ya bi bayan matasan wadanda ko riga babu a jikinsu. Nan da nan dan damben ya bayyana bidiyon inda mutane da dama suka dinga mamaki.
Mutane dayawa sun dinga tsokaci iri-iri karkashin wallafar ta shi, wadanda suka ce bayan ganin dan damben ne barayin suka tsere don gudun su ci na jaki.
Duk da dai babu wanda ya kama a cikinsu, amma jin ya biyo su ne ya sanya suka fasa satar suka gudu.
Satar mai: Buhari ya sake ba da sabon umarni ga hukumomin tsaro
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin tsaro da su kawo karshen satar danyen mai kafin ranar 29 ga watan Mayu.
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva ne ya bayar da wannan umarni yayin da yake jawabi ga sojojin Operation Delta Safe.