An bayyana sunayen manyan ‘yan wasa biyar da ka iya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana,Daily Post ta rawaito.
Kyautar Ballon d’Or ta kasance kyautar mutum daya da aka fi badawa ga ‘yan wasan kwallon kafa kuma Mujallar labaran Faransa ‘France Football’ ce ke bayar da ita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Messi Ya Mayar Da Martani Yayin Da dan Wasan Barcelona Zai Bar Kungiyar
Kyautar da ta fi kowane mutum daraja a ƙwallon ƙafa yanzu ana ba da ita ga mafi kyawun dan wasan ƙwallon ƙafa daya fi iya taka leda a kakar wasa.
Kwamitin ‘yan jaridu na kasa da kasa, kyaftin din tawagar kasa da masu horar da ‘yan wasa ne ke zaban wanda ya yi nasara.
A cewar Sportskeeda, ‘yan wasa biyar da ka iya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana sune:
Victor Osimhen (Nigeria/Napoli)
Vinicius Junior (Real Madrid/Brazil)
Kylian Mbappe (Faransa/PSG)
Lionel Messi (Argentina/PSG)
Erling Haaland (Norway/Manchester City)
A wani labarin kuma,Da Yuwuwar Yan wasan Barcelona Biyu, Su bi Messi Zuwa Sabuwar Kungiyarsa
Al-Hilal na fatan zawarcin Lionel Messi daga Paris Saint-Germain a wannan bazarar, ta hanyar kulla yarjejeniya da takwarorinsa na Barcelona Sergio Busquets da Jordi Alba. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
An yi imanin cewa kungiyar ta dake buga gasar Saudi Pro League ta gabatar da kudin da ya kai fam miliyan 400 ga Messi, wanda ke shirin zama wakili na kyauta.
Ba a tsammanin kyaftin din Argentina zai kulla sabuwar yarjejeniya da PSG.
A cewar El Chiringuito, Messi ya shirya karbar tayin Al-Hilal.
An kuma yi ikirarin cewa dan wasan da ya lashe kofin duniya Busquets zai amince da kwantiragin shekaru biyu a kungiyar dake Gabas ta Tsakiya idan kwantiraginsa ya kare a Barcelona.