Wata mata matashiyar budurwa ƴar Najeriya, @bims_luxury, ta janyo mutane da dama sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi a kanta a manhajar TikTok, bayan ta nuna mijinta.
Matashiyar budurwar da ita da mijin nata suna sanye ne da kaya iri ɗaya. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Zargin Tinubu Da Shaidar Zama Dan Ƙasa Biyu Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Najeriya
A farkon bidiyon, budurwar tana zaune aka wata luntsumemiyar kujera yayin da mijin nata ya zauna a akan hannun kujerar.
Sauran hotunan cikin bidiyon sun nuna su tare a matsayin ma’aurata. Sun yi matuƙar kyau sosai.
Mutane da dama sun yi ta maganganu akan bidiyon a wajen yin sharhi da ke a ƙasa.
Daga cikin waɗanda suka yi magana akan bidiyon, akwai masu yi mu su fatan samun rayuwar aure mai albarka.
Ku kalli bidiyon a nan
Bidiyon ya yaɗu sosai, wanda ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, sama da mutum 500 suka yi sharhi akan sa, inda sama da mutum 15,000 suka danna masa alamar ‘like’
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
Afunkybaby ta rubuta:
“Ƴar’uwa na taya ki murna sosai oooo, na rantse irin waɗannan tsofaffin sun fi kula wa da mutum ba irin samarin yanzu ba.”
@Raufuabiola99 ya rubuta:
“Kuɗi na magana”
BURLINGTON ya rubuta:
“Abinda ya fi muhimmanci shine ra’ayin ta ba wai maganganun banza da mutane ke yi ba.”
Istijabahzee1 ta rubuta:
“Idan dai har tana cikin farin ciki.”
Adun Olami ta rubuta:
“Ina taya ki murna, Allah ya albarkaci auren ku.”
Bidiyon Dattijo Mai Shekara 101 Da Diyarsa Mai Shekara 81 Ya Dauki Hankula Sosai
Masu amfani da manhajar TikTok sun yi tsokaci mai kyau kan bidiyon wani dattijo da ɗiyar sa.
A cikin bidiyon wanda wata mai amfani da @babylove20000000 ta sanya, an bayyana cewa dattijon shekarun sa ɗari da ɗaya a duniya (101).